Wednesday 1 June 2016

Babban Bankin Musuluncin AGM 2015


A jiyane babban Bankin Musulunci na farko a kasarnan wato Ja'iz Bank Plc ya gabatar da taron shekara Dubu Biyu dasha Biyar 2015 wanda Shugaban Bankin Chairman Alh Dr. Umaru Mutallab CON ya Jagoranta, Taron wanda yagabata a Babban Dakin Taro na Shehu Musa YarAdua Centre dake Birnin Tarayya Abuja. wanda a wajen taron masu hannun Jari a Bankin suka bukaci a sake nada sabbin Darabtoci, cikin ikon ALLAH Mai Girma Alh Dr. Umaru Kwairanga (Sarkin Fulanin Gombe) aka kara zabanshi a karo nabiyu domin ya cikin Darabtoci, Hakazalika mafi yawancin wadanda suka sami damar magana a dakin taron sunjinjinawa Darabtocin abisa irin jajircewa da kuma sadaukar dakai dasuke domin ganin Bankin yacigaba kuma da yanayin yanda masu Ajiyar Kudi, Kasuwanci, Riba dakuma samun Lasisi da Bankin yayi daga Babban Bankin Kasa wato Central Bank of Nigeria CBN, da hannun Jari da Bankin yake samu a koyaushe dadai sauransu. yasami halartan manyan Mutane kuma Jagororin Al Umma kamar Shugaban Kungiyar Jamaatu Izalatul Bidi'a Wa'ikamatis Sunnah As Shaikh Abdullahi Bala Lau dadai sauransu,
Buguda kari masu hannayen jarin dasuka sami damar yinbani sunkara Jinjina ta musamman ga Babban Darabta Alh Dr. Umaru Kwairanga (Sarkin Fulanin Gombe) dangane da irin Sadaukar dakai dayake wajen ganin Bankin takaiga Nasara ta fannoni da dama musamman bangaren dayake Jagoranta.

daga karshe, mafi yawancin masu RUWA da tsaki da masu hannun Jari a Bankin sunyi jinjina da fatan Alkhairi ga Alh Dr. UMARU KWAIRANGA Sarkin Fulanin Gombe a wajen taron sabida jin irin tarihinshi da aka bayyana a wajen taron na irin kwarewarshi da gogewa dayayi akan harkan Kasuwanci da tattalin Arzikin Kasa anan dakuma irin alakan dayakeda ita da manya manyan Kamfanoni na kasa Najeriya dama Kasashen Duniya.
muna yima ALLAH Godiya marar adadi,

 ALLAH yamana Jagora
ALLAH yakara Daukaka Umaru Kwairanga
ALLAH yakara Daukaka Ja'iz Bank
ALLAH yakara Daukaka Nyaeriya

No comments:

Post a Comment

MUNSAYO FORM NA TAKARAN GWAMNAN GOMBE DOMIN KAWO CANJI A JIHAR GOMBE A 2019 INSHA ALLAH

ALHAMDULILLAH Da safiyar jiya Juma'at 07-09-2018 Mai Girma Alh Dr. UMARU Kwairanga (Sarkin Fulanin Gombe) tare da Tawagarshi mukaje ...