A yammacin ranar Lahadi 19 Febrairu 2017 a Babban Birnin Tarayya Abuja aka Gudanar da Taron ISA WALI Empowerment Initiative Foundation wanda ya gudana a Babban Dakin Taron na Yar'adua Centre Taron yasami Halartan Manyan Mutane dake Jagoranci a Kasarmu irinsu Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya kuma Shugaban Kasa mai rikon Gado Farfesa Yemi Osibanjo, Sarkin Kano Mal. HRH Sanusi Lamido Sanusi, Tsohon Shugaban Alkalai na Kasa Justice Uwais, Hamshakin Dankasuwannan Alh Dr. Umaru Mutallab, Alh Ahmed Joda, Minista Amina, dakuma Jagoran Alkhairi Alh Dr. Umaru Kwairanga (Sarkin Fulanin Gombe)
Mai Gidauniyar Al Alkhairi Sarkin Fulanin Gombe Foundation wanda a Tarihin Jihar Gombe Alh Dr. Umaru Kwairanga (Sarkin Fulanin Gombe) shine Mutum na farko daya fara kirkiran irin wannan Gidauniya domin Tallafawa masu kananan karfi kama saga Mata masu Juna Biyu, samarwa Matasa Ayyukanyi, Daukar nauyin Yara Marayu suyi karatu domin samun Rayuwa kyau, Tallafawa Asubitoci da Magani dadai sauransu.
Muna Addu'ar ALLAH yakarama Rayuwar Alh Dr. UMARU KWAIRANGA Sarkin Fulanin Gombe Albarka, ALLAH yashiga Lamuranshi yakaramar Girma da Daukaka a idon Duniya, yamar Jagora yabiyamar dukkan Bukatunshi na Alkhairi Duniya da Lahira kuma ALLAH ya karbi Addu'o'inmu na Alkhairi.
No comments:
Post a Comment