Thursday, 29 December 2016

UMARU KWAIRANGA MAI DOGARO DA IKON ALLAH

ALKHAIRI SABONE WANDA YASABA BAZAI IYA DENAWABA

Kàmar kullum dai Mai Girma Alh (Dr) Umaru Kwairanga (Sarkin Fulanin Gombe) Jagoran Alkhairi yasayo Motocin tona Bore hole ga Gidauniyarshi mai suna Sarkin Fulani Foundation don wadatar da Al Ummarshi da Ruwan Sha a lungu da sako dake fadin Jihar Gombe duba da irin fama da muke da rashin Ruwa a fadin Jihar Gombe.

idan bamu mantaba a bangaren LAFIYA wannar Gidauniya ta Mai Girma Sarkin Fulanin Gombe tana iyaka kokarinta don samar da sassaucin Rayuwa ga Al Ummar Jihar Gombe domin abaya bayannan taketa zagayawa Asubitocin dake fadin Jihar Gombe don rabawa Mata masu juna biyu kayan karbar Haihuwa duba da irin yanayin da Kasa take ciki

Hakazalika tayi bangaren ILIMI wannar Gidauniya ta Mai Girma Sarkin Fulanin Gombe ta taka rawar gani ga Dalibai Yayan Jihar Gombe wanjen rabamusu Katin JAMB don samun damar rubuta jarabawar shiga Makarantar gabada Sakandare, bata tsaya ananba ta raba Tallafin kudin Rijistar shiga Makarantar Jami'a ga Dalibai masu karamin karfi donta Gina Rayuwar Al Umma

SAMAR DA AYYUKANYI GA MATASA bugu da kari daga shekaru Uku zuwa hudu da suka gabata zuwa yanzu yasamawa Matasa Yayan Jihar Gombe a Kalla 520 Aikinyi a wurare daban daban batare da yasansuba wanda dukkansu yanzu suna wuraren daya sama musu, wanda Alhamdulillah ganin irin wannan Hobbasa da wannan Gidauniya mai suna Sarkin Fulani Foundation wacce shi Alh (Dr) Umaru Kwairanga takeyi yasa wasu daga cikin manyan Jihar Gombe suka kirkiri tasu Gidauniya don suma suyi koyi da Halin kwarai irinna Mai Girma Alh (Dr) Umaru Kwairanga (Sarkin Fulanin Gombe)

Da wannan muke godiya ga ALLAH (SWT) daya Azurta Jiharmu ta Gombe da samun Mutum mai kishin Al Ummarshi wato Alh (Dr) UMARU Kwairanga (Sarkin Fulanin Gombe) muna Addu'ar ALLAH yakarama Rayuwarshi Zuriyarshi da Dukiyarshi Albarka kuma yabiyamar dukkan Bukatunshi Duniya da Lahira

No comments:

Post a Comment

MUNSAYO FORM NA TAKARAN GWAMNAN GOMBE DOMIN KAWO CANJI A JIHAR GOMBE A 2019 INSHA ALLAH

ALHAMDULILLAH Da safiyar jiya Juma'at 07-09-2018 Mai Girma Alh Dr. UMARU Kwairanga (Sarkin Fulanin Gombe) tare da Tawagarshi mukaje ...