ASHAKACEM LOKACIN UMARU KWAIRANGA: WANI YANATA HARBIN ISKA.
Shati fadi da wani yakeyi akan abinda bashida masaniya akai kokadan, dukda cewar babu bukatar amsamar akan wannan Maganan amma akwai bukatar karin haske saboda mutane sufahimci hakikanin Gaskiyan lamarin. bazanyi wannan bayani kare Umaru Kwairanga ba, amma kasancewar inada cikekken masaniya a lokacin da yake rike da Shugabancin Darabtoci na Kamfanin AshakaCem (Chairman Board of Directors of AshakaCem), wannan daliline yasa naga yadace irin Ayyukan Alkhairi daya shuka a Kamfani da kuma Garuruwan dake mallakar wannan yakin kai tsaye, sabida makaranta sugane Gaskiya, abun mamaki saiga wani yakasa yabama wannan Dan kasa Nagari, Haziki mai kishin yankinmu na Gombe, wanda yayi iya kokarinshi wajen ganin ya ciyar da Rayuwar Al Ummar wannan yanki na AshakaCem gaba. wanda yacire duk wani shakka don ganin ya tabbatar da Gaskiya, wanda ahikadai ne yasan dalilinsa nayin hakan, a shekarun da Kwairanga yake Shugabantar Kamfanin AshakaCem a matsayin (Chairman Board of Directors) yayi abubuwa da dama nagani nafada wanda nashaida, wannan wanda yake ta magana bai taba aiki da wannan Kamfani AshakaCem ba kuma baitaba kawomar koda Ziyara sau dayaba a sanina duk fadefaden dayakeyi yanayine kawai batare da wata shaida ko madafaba akan wadannan Maganganu daga cikin Ayyukan Alkhairi daya gabatar a lokacin dayake shugabancin Kamfani sunhada da.
KAURA DA KAUYUKA DOMIN SAMUN NATSUWA:
Wadansu Kauyuka dasuke zaune kusa da Kamfanin AshakaCem shekaru aru aru baya, sunsha wahala sosai dangane da Nakiya da Kamfani take yawanyi a kusa da kauyukan. Wanda sanadiyyar kara yawan Nakiyoyin yasa hartakai ga suna fuskantar barazanar tsatstsagewar Gidajensu hartakai ga suna samun matsalan ciwon kunne sundau shekara masu yawa suna korafi ga Shugabannin Kamfanin AshakaCem baa saurari kokensuba haka sukaci gaba da zama cikin Dardar, a kullum mafarkinsu shine Kamfani tacanja musu matsuguni, mafarkinsu bai zama Gaskiya ba saida ALLAH yakawo Umaru Kwairanga matsayin Babban Darabtan Kamfani wanda sannu a hankali yazo matsayin Shugaban Bod na Kamfani. ya tsaya tsayin daka don ganin ya tabbatar da an Gina sabbin Gidaje, Makarantar yara da kuma Asibiti domin wadannan kyautuka su koma don samun Natsuwa. hakan yasanya Al Ummar wannan yanki Farin ciki da Jindadi matuka a lokacin daya fara saka tubalin wannan Ginin kuma bayan watanni Tara (9) yadawo domin ganin yarabawa Al Ummar wadannan kyautuka yan Makullen sabbin Gidajen da aka gina musu, yanzu ana kiran Kauyen LADDE BAGE gaduk mai sha'awar ya tabbatar da hakan zai iya zuwa.
KARA GIRMAN KAMFANIN ASHAKACEM:
Duba da yanayin karancin Siminti da Kamfanin take iya samarwa na Ton 1 Miliyan, hakan yasa Kwairanga da Dabtocin sa dasuke Jagorantar Kamfani, yakawo shawaran yakamata a kara Girman Kamfani domin samar da Isasshen Siminti ga Masu saye da sayarwa, domin idan akayi wannan fadada Kamfani aka gama Kamfani zatana iya samarda Ton Miliyan 3.5 Uku da rabi. kuma Kwairanga ya Jagoranci Shugabannin Kamfanin AshakaCem zuwa wajen Shugaban kasa na wancan lokacin wato Good lock Jonathan suka Tattauna kuma ya amince da wannan bukatar da sukeda ita, kuma yaturo Ministan Kamfanoni na wancan Lokacin wato, Olusegun Aganga domin ya dasa tubalin Fadada wannan Kamfanin wanda tun daga wancan Lokacin zuwa yanzu babu labarin wannan Aikin sabida wanda yafara don ganin an samar da Ayyukanyi wa Al Umma kuma Kamfani takara karfi wajen samin kudin shiga amma shiru kakeji babu labarinshi.
SAMAR DA MANYA MANYAN MADAFUN IKON KAMFANIN:
A lokacin da kokarin mutum a wajen canjin Ofishi ya zamto yana wahalan gaske domin idan mutum yabar ofiahin da yake to sai a dauko wani daga wajen wannan Sashin Ma'aikata domin ya maye gurbinshi koda baisan wannan Aikinba, sai lokacin da Kwairanga yazo matsayin Shugaban Kamfanin AshakaCem ne yakawo canji kuma a matsayinshi na mai Kishin Yankinshi lokacinshine aka fara samun Manyan Darabtoci har Mutum Uku (3) 'Yayan Jihar Gombe wanda suka hada da Dr. Abubakar Ali Gombe, Mai Girma ALH Abubakar Kwairanga (Sarkin Funakaye) da kuma shi kansa Uban gayya Alh Dr. Umaru Kwairanga (Sarkin Fulanin Gombe) Shugaban Darabtocin Kamfanin AshakaCem hakazalika yakawo Mutum Uku 3 'Yayan Jihar Gombe a matsayin Manajoji na kololuwa wanda yahada da Yusuf Lamuwa Nafada (Manager Finance), Hajiya Hauwa Baba Ahmed Billiri (Manager Human Resources) Alh Salisu Ajiya Kwami (Sales and Maketing) wanda biyu (2) daga ciki wato Salisu Ajiya, Hauwa Baba Ahmed wannan Kujerun basu tabbataba kasantuwar kokarin a cusa wadansu daga wani bangare saida Umaru Kwairanga ya tsaya tsayin daka don ganin ya tabbatar da Adalci kuma ya tabbatar musu da Kujerunsu wannan dalilin shine yajawo jinkirin basu matsayin.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
MUNSAYO FORM NA TAKARAN GWAMNAN GOMBE DOMIN KAWO CANJI A JIHAR GOMBE A 2019 INSHA ALLAH
ALHAMDULILLAH Da safiyar jiya Juma'at 07-09-2018 Mai Girma Alh Dr. UMARU Kwairanga (Sarkin Fulanin Gombe) tare da Tawagarshi mukaje ...
-
We want use this medium to Congratulate our Sister Hajia Farida Kwairanga the Daughter of the future Governor of Gombe State 2019 Insha AL...
-
ALHAMDULILLAH Da safiyar jiya Juma'at 07-09-2018 Mai Girma Alh Dr. UMARU Kwairanga (Sarkin Fulanin Gombe) tare da Tawagarshi mukaje ...
-
Gombe - Day New Sarkin Fulani Was Turbanned The event of Saturday, January 10, 2009 in Gombe, will forever linger in the minds of G...
-
Yakubu Ahmed Bangu Wrote: FOR THE BENEFIT OF THOSE WHO DONT KNOW ALH. DR UMARU KWAIRANGA (SARKIN FULANIN GOMBE). WHO IS DR UMARU KWAIRA...
-
[True Story] “After performing Salat Al Maghrib, she put her make-up, wore her beautiful white dress preparing herself for her wedding pa...
No comments:
Post a Comment